24 Afirilu 2026 - 23:34
Source: ABNA24
Ƙasa Da Shekaru 6 Amurka Ba Zasu Iya Maye Gurbin Harsashen Da Ta Lalata Su A Yaƙi Da Iran Ba

Rahotonnin tsaron Maƙiya sun fitar cewa zai iya ɗaukar har zuwa shekaru shida kafin a maye gurbin dukkan harsasan da aka yi amfani da su a yaƙin da ake yi da Iran. 

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Jaridar Wall Street Journal, wadda ta ambato jami'an Amurka, ta ruwaito wani mummunan yanayi da ba a taɓa gani ba a kan tarin makamai masu linzami da na tsaro na Amurka da ke tabbatar da "Karancin harsasai da yaƙin da aka yi da Iran ya haifar na iya raunana ikon na kariyar Taiwan daga duk wani hari na China.

Sojojin Amurka sun harba makamai masu linzami na Tomahawk sama da dubu tun farkon yaƙin." "Tsakanin makamai masu linzami 1,500 zuwa 2,000 sun kuma yi amfani da su tun farkon rikicin da Iran ne wanda ke iya ɗaukar har zuwa shekaru shida don maye gurbin harsasan da aka barnata gaba ɗaya.

Your Comment

You are replying to: .
captcha